Isa ga babban shafi
Japan

Japan na shirin ware miliyan 7.7 na Dalar Amurka domin kasashen Afrika

Gwamantin kasar Japan na shirin sanar da wani gagarunim shiri, da zai tanadi Dalar Amurka miliyan 7,700 domin habaka tattalin arzikin kasashen Afirka.

Firaministan Japan, Shinzo Abe
Firaministan Japan, Shinzo Abe Reuters
Talla

Kafafen yada labaran kasar ta Japan, sun ce a gobe Asabar ne Firaministan kasar, Shinzo Abe zai sanar da hakan a lokacin taron shekara shekara da ake gudanarwa tsakanin Japan da kuma kasashen Afirka wanda zai gudana a birnin Tokyo.

Bayan taron na birnin Tokyo, Abe da kuma wakilan sauran kasashe, har ila yau za su halarci wani taro na shekara shekara kan raya kasashen Afirka da zai gudana a birnin Yokohoma na tsawon kwanaki uku.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.