Isa ga babban shafi
Turkiya-Qatar

Turkiya ta bayar da goyon baya zuwa Qatar

Shugaban Turkiya Recep Tayip Erdogan a jiya juma’a ya tabbatar da goyan bayan kasar sa zuwa hukumomin Qatar,inda ya ci gaba da cewa duk da nuna rashin amincewar kasashen larabawa, Turkiya ba zata canza manufofin da take da su da Qatar.

Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiya
Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiya ADEM ALTAN / AFP
Talla

Shugaba Erdogan da babbar murya ya tabbatar da cewa babu wata sheida da yake da ita a hannun sa dake nuna masa cewa Qatar ta tallafawa wasu kungiyoyin yan ta’ada.

A karshe ya yi kira zuwa kasashen da suka nuna yanke hulda da Qatar da sun canza wannan siyasa ta su .
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.