Isa ga babban shafi
Lebanon

Damuwar Majalisar Dinkin Duniya dangane da Lebanon

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kasashen Duniya su mayar da hankali ga kasar Lebanon, tareda bayar da agaji da zai taimaka don rage radadin da yan kasar ke fama da shi bayan fashewar da ta wakana ranar talata a Beirut.

Tashar jirgin ruwan Beirut da aka samu fashewa a ranar talata
Tashar jirgin ruwan Beirut da aka samu fashewa a ranar talata REUTERS/Issam Abdallah
Talla

Kokarin Majalisar dinkin Duniya don ganin kasashen Duniya sun kai dauki ga Lebanon, bayan wata fashewa da ta lakume kusan rabbin babban birnin Beirut tareda haddasa mutuwar mutane da dama, hukumar ta shigar da wannan kira, a lokacin da hukumar lafiya ta Duniya a daya geffen ta na mai bayyana cewa ta na bukatar akala milyan 15 na dalla, bayan haka hukumar kula da kuma kare hakokin yara ta Unicef ta ce a nata bangaren ta na mai bukatar milyan 8 da digo 2 na dalla ,kudaden da za su taimaka don magance bukatun jama’a a wannan yanayi na jimami.

Wadanan hukumomin sun bukaci a gaggauta kai dauki kasar ta Lebanon, kasar da mutanen ta ke rayyuwa cikin wani yanayi na wahala.

Bukatun na da yawan gaske a cewar wani jami’in hukumar Unicef Marixi Mercado, wanda ya bayyana cewa a zaman da ake yanzu haka kusan yara dubu 100 suka samun kan su a jerrin yan gudun hijira..

Hukumar ta Unicef na sa ran tara kusan milyan 8 na dalla.

Hukumar lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa asibitoci sun batse da marasa lafiya da suka hada da mutanen da suka samu rauni bayan fashewar a Beirut, kazalika wasu asibitocin sun ruguje .

Kasar ta Lebanon na yo odar kusan kashi 85 cikin dari na abincin da jama’ar ta ke ci daga waje.

Hukumar abinci ta Duniya a karshe ta bayyana cewa akala ana bukatar rabawa jama’a a kwanon abici dubu 5000 .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.