Isa ga babban shafi
Duniya

An cafke tsohon shugaban kasar Honduras

Jami’an tsaro a filin tashi da saukar jirage na Tegucigalpa dake kasar Honduras sun cafke tsohon Shugaban kasar Manuel Zelaya dauke da kusan dalla dubu 18 a lokacin da yake shirin barin kasar zuwa Mexico.

Tsohon Shugaban kasar Honduras- Manuel Zelaya
Tsohon Shugaban kasar Honduras- Manuel Zelaya RFI
Talla

Dan siyasar ya bayyana cewa ba shi da masanniya dangane da kudin da aka samu a jakar sa.

Samun sa da takarddar kudi da bai bayyanawa masu bincike da farko ba, laifin  ne a kasar ta Honduras.

Bayan tsare tsohon Shugaban kasar na wani lokaci ,jami’an tsaro sun sallame shi,tareda baiwa masu bincike ci gaba da gudanar da bincike don gano gaskiyar lamarin.

Tsohon Shugaban kasar na daga cikin mutanen da yanzu haka ake kalo a matsayin masu adawa da tsarin hukumomin dake rike da madafan ikon kasar ta Honduras yanzu haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.