Isa ga babban shafi
Faransa

An sake gano wani mutun mai dauke sabon nau’in cutar Korona a Faransa

Ma’aikatar lafiyar Faransa ta sanar da gano mutum guda da ya kamu da sabon nau’in cutar Korona mai saurin yaduwa da ya samo asali daga kasar Afrika ta Kudu.

Wuraren gudanar da gwajin mutanen da suka kamu da cutar Covid 19
Wuraren gudanar da gwajin mutanen da suka kamu da cutar Covid 19 REUTERS/Benoit Tessier
Talla

Bayanai sun ce mutumin ya dawo daga balaguron da yayi zuwa Afrika ta Kudun ne inda ake kyautata zaton ya kamu da cutar.

Karo farko kenan da sabon nau’in cutar ta bulla a Faransa, wadda tuni ta yadu zuwa wasu kasashe, ciki harda Birtaniya, jamus, Spain da kuma Japan.

A kasar ta Faransa kungiyoyi sun soma bayyana damuwa ganin karancin mutanen da yanzu haka aka yiwa allurar rigakafin kamuwa da cutar Coronavirus. Mutane 200 ne aka yiwa allurar Korona a Faransa

Wasu alkaluma daga sashen kiwon lafiyar Turai na nuni cewa a Jamus kadai mutane 42.000 ne suka amfana da allurar yanzu haka,Birtaniya mutane 900.000 sai Faransa mutane 200 kacal.

Daya daga cikin yan majalisu na kasar ta Faransa bangaren masu mulki Bruno Retailleau ,ya rubuta a shafin sa na twitter cewa kamata gwamnati ta fitar da jadawalin da likitoci za su yi amfani da shi don yiwa jama’a allurar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.