Isa ga babban shafi
Asiya

Iran ta kaddamar da soma aikin tace sanadarin l'uranium

Iran ta kaddamar da soma aikin tace sanadarin l'uranium zuwa kashi 20% a cibiyar samar da nukliyarta ta karkashin kasa dake Fordo, matakin na farko na yinkurin watsi da yarjejeniyar nukliyar da ta cimma da kasashen duniya, da kuma ke zuwa a dai dai lokacin da take tsakiyar tada jijiyoyin wuya tsakaninta da Amruka.

Sashen makamashin Nukiliyar Iran
Sashen makamashin Nukiliyar Iran AFP
Talla

A yau litanin dakarun juyin juya halin musuluncin kasar ta Iran sun bayyana kama wani jirginruwan dakon manfetur na kasar koriya ta kudu a matsigin Golf, inda aka baza jiragen ruwan Amruka tuni dai mahukumtan Séoul suka bukaci sakin jirgin

A watan mayun 2019 shekaru guda bayan da amruka ta janye daga yarjejeniyar nukliyar Iran ta 2015 tare da ma yar da jerin takunkuman kariyar tattalin arzikin da ta kakabawa kasar yanzu haka dai iran ta fara janywa daga alkawulan da ta dauka na mutunta yarjejeniyar.

Amruka da Isarela dai na zargin kasar Iran ne wace suka danganta a matsayin makiyarsu ta damba daya da kokarin mallakar makman nukliya zargin da tuni Iran ta sha musantawa.

Kokarin inganta sanadarin Uraniyom zuwa kashi 20% ya rigay ya fara a cibiyar tace sanadarin dake Shahid Alimohammadi (Fordo)",kilo mita 180 kudancin Téhéran, babban birnin kasar kamar yadda kakakin gwamnatin kasar Ali Rabii ya sanar a tashar talabijin dun gwamnatin kasar,

A cewarsa shugaban kasar Hassan Rohani ne ya bada umarnin soma aikin inda yanzu haka yan awowin da suka gabata aka fara aikin zuba gaz na soma tatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.