Isa ga babban shafi
Amurka

Ana ci gaba da samun yawaitar masu dauke da Covid 19 a Amurka

Hukumomin China suka tsaurara matakan kariya wajen hana cigaba da yaduwar annobar coronavirus, Amurka ta ce tilas kowanne matafiyi da zai shiga kasarta yayi gwajin cutar dan tabbatar da lafiyarsa, ganin cewa a cikin kwana guda adadin wadanda suka mutu bayan harbuwa da cutar ya kai 4,500.

Kwayar cutar coronavirus da aka yi amfani da na'urar komfuta wajen fitar da taswirar ta
Kwayar cutar coronavirus da aka yi amfani da na'urar komfuta wajen fitar da taswirar ta NEXU Science Communication | Reuters
Talla

Karo na farko da Amurka ta samu adadi mafi yawa na mutanen da suka mutu bayan sun kamu da cutar covid19, adadin da ya haura 4000 a cikin kasa da sa’oi 24.

Kididdigar Jami’ar John Hopkins ya bayyana cewar a cikin sa’a guda kawai an samu sabbin mutane sama da dubu 235 da suka harbu da cutar bayaga wasu 4,470 da suka mutu.

Amurka na fuskantar barazana daga cutar saboda yadda take ruruwa a kasashen duniya tamkar wutar daji, ta sanar a yau cewar duk wanda zai shiga Kasarta dole ya nuna shaidar gwajin cutar da yayi dan tabbatar da lafiyar jikinsa.

Tun bayan bullar annobar cutar kawo yanzu, akalla mutane miliyan 22 da dubu 800 ne suka harbu da cutar a Amurka baya ga wasu dubu 380 da suka mutu a kasar mafi karfin tattalin arziki a Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.