Isa ga babban shafi
Afrika

Shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita ya ziyarci Sevare

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaran sa na Kamaru sunyi allah wadai da harin da kungiyar jihadi ta kai zuwa cibiyar rundunar tsaro ta G5 a garin Sevare dake kasar Mali.

Dakarun G5 a arewacin kasar Mali
Dakarun G5 a arewacin kasar Mali © AFP
Talla

Shugaba Emmanuel Macron da ya gana ta wayar talho da Shugaban Kamaru sun ambato yanayin tabarbarewa tsaro da ake fama da shi a yankin tafkin Chadi tareda bukatar ganin sun hada karfi domin kawo karshen wanan yanayi.

Harin Sevare a kasar Mali ya yi sanadiyar mutuwar mutane shida a cewar tashar talabijen na France 24 kwanaki kadan da soma gagarumin taron kungiyar kasashen Afrika a Mauritania, inda ake sa ran Shugabanin kasashen za su tattaunawa da Shugaban Faransa dangane da yanayin tsaro a yankin.

Shugaba Mali Ibrahim Boubacar Keita ya sha alwashin murkushe yan ta'adda masu kai hari a kasar ta Mali.

Rundunar G5 Sahel dai rundunar hadin gwiwa ce ta kasashen Mali Nijar Chadi, Mauritania da kuma Burkina Faso wadda ke samun tallafin Faransa dama Majalisar Dinkin Duniya don yaki da ta'addanci a yankin na Sahel.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.