rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Ilimi Amurka India

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Ya'yan talakawa na fama da dakikanci- Bincike

media
Ana samun kimanin yara miliyan 250 a sassan duniya da basirarsu bata habbaka a kowacce shekara, in ji masana. AFP PHOTO / ANDREEA CAMPEANU

Wani sabon bincike ya nuna cewa, kananan yara da aka haifa cikin talauci kuma iyayensu ke da karancin ilimi, na fama da rashin kaifin basira, sabanin takwarorinsu da suka fito daga gidajen masu arziki.


Tawagar masu binciken karkashin jagorancin, Farfesa John Spencer na jami’ar East Anglia, ta gudanar da nazarinta kan kwakwaluwar yara daga wata hudu zuwa shekara hudu a India.

Tawagar ta kwatanta kwakwaluwar yaran talakawan na India da kuma takwarorinsu na jihohin arewacin Amurka, in da ta gano cewa, ‘ya’yan talakawan na da toshewar basira, sannan basa mayar da hankali wajen karatu.

Tawagar ta Farfesa Spencer ta ce, a kowacce shekara ana samun yara kimanin miliyan 250 da kwakwaluwarsu bata habbaka a kasashe matalauta.

A cewar tawagar, akwai bukatar gaggawa kan gudanar da bincike game da illar talauci ga kaifin basira.