Isa ga babban shafi
Mata

Illar laulayin safe ga masu junan Biyu

Wani rahoto da masu bincike kan kiwon lafiya suka fitar, ya ce laulayin da mata masu juna biyu ke yi da sanyin safe na taka rawa wajen zubewar ciki.

Masana sun ce laulayi tsakanin mata masu junan biyu na haifar da barinsa
Masana sun ce laulayi tsakanin mata masu junan biyu na haifar da barinsa GettyImage/Klassen Images
Talla

Jaridar kiwon lafiyar Amurka, ta rawaito cewa, Tsakanin kashi 50 da 80 na mata masu junan biyu, da ke yawaita laulayi da amai a matakin farko na samun ciki musamaman da sanyi safe ko cikin dare, su suka fi fuskantar barazanar barewar ciki.

A cewar jaridar, bincike da kwararrun likitoci a Amurka suka gudanarwa kan mata 797 da ke dauke da junan biyu, ya tabbatar da cewa kashi 75 sunyi bari sakamakon wadanan kananan cuttuka da akasarin masu ciki ke yi.

Masanan sun ce yawan laulayi da amai na hana mata masu ciki cin abinci, wanda hakan ke matukar tasiri kan abin da suke dauke da shi.

Bincike ya kuma bayyana yadda rashin cin abinci ke jawo karancin sinadari Insulin da girma mahaif.

Sai dai bincike bai bayar da bayyanai kan matakan da za a dauka ko a bi wajen rage yawan laulayi ko amai da ake samu tsakanin akasarin mata da ke dauke da junan biyu a matakin farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.