rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Lafiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

''Amfani da kai a kwallo na haifar da ciwon mantuwa''

media
Amfani da kai a wasanni kwallon kafa na haifar da ciwon mantuwa a cewar masana

Wani bincike masana kiwon lafiya, ya ce kwararun ‘yan wasan kwallon kafa na fuskantar barazanar kamuwa da Cutar kwakwalwa da ke haddasa mantuwa, kuma ciwon mantuwa ciwo ne da ke aka fi samu tsakanin ‘yan wasan dambe da kwallon kafa.


Binciken da aka wallafa a wata mujallar kiwon lafiya, ya yi nazari ne kan tsoffin ‘yan wasa kwallon kafa 14 da ke dauke da ciwon mantuwa, wanda kuma suka soma kwallon tun suna da kananan shekaru da kuma yawaita amfani da kai a buga kwallo.

‘Yan wasan da ba a wallafa sunayensu ba, fittatune da akasari suka shafe shekaru 26 suna taka leda. Daga ciki akwai wadanda suka ta ba yi wa Swansea da South Wales wasa a tsakanin 1980-2010.

Bincike ya ce gwajin da aka gudanar kan shida daga cikin ‘yan wasa, ya bayyana cewa hudu na cikin hali mai tsananni na mantuwa, wanda ciwo ne da ake iya samu tsakanin kashi 12 cikin 100 na al’umma kacal.

A cewar shugabar Binciken da ke kwallajen London Institute of Neurology, Helen Ling, wannan ya nuna karara alakar da ke akwai tsakanin wasanni kwallon kafa da ciwon mantuwa mafi muni da ake kira ''Chronic Traumatic encephalopathy'' a Turance.

Ling ta ce wannan batu ya bijiro da bukatar tuntubar hukumomin kwallon kafa na FA da FIFA don samar da mafita cikin gaggawa.

Ling ta ci gaba da bayyana cewa alamomin ciwon mantuwa na soma bayyana ne daga shekaru 60 tsakanin masu kwallon kafa sabanni shekaru 70 da aka saba gani tsakanin sauran al’umma. Kuma 12 cikin 14 na mutuwa saboda wannan ciwon idan ya yi tsanani.

A karon farko kenan da ake danganta kwallon kafa da ‘yan wasa ke yi da kai a matsayin musababbin ciwon mantuwa.