Isa ga babban shafi
lafiya

Magungunan tarin fuka ba sa aiki

A daidai lokacin da ake tunawa da ranar yaki da cutar TB ko kuma tarin fuka a duniya a wannan juma’a, masana kiwon lafiya sun ce wasu daga cikin sabbin magungunan da ake amfani da su domin warkar da cutar ba za su yi amfani ga masu fama da larurar ba, musamman idan aka yi kuskure wajen yin amfani da su.

Tarin fuka ya kashe mutane kimanin miliyan daya da dubu dari takwas a shekarar 2015.
Tarin fuka ya kashe mutane kimanin miliyan daya da dubu dari takwas a shekarar 2015. Crédit : Getty Images/ David Rochkind
Talla

Rahoton wanda aka fitar a jajibirin ranar yaki da cutar ta tarin TB a duniya, ya ce an kara gano wasu magunguna kamar bedaquiline, delamanid da kuma linezolid domin fada da wannan cutar.

To sai dai masana kiwon lafiya sun ce akwai bukatar kara fadakar da jama’a dangane da yadda ake amfani da wadannan magunguna, kuma idan aka ci gaba da shan su akan kuskure za a iya a wayi gari ba su da wani tasiri wajen warkar da Jama'a.

Rahoton wanda cibiyar bincike kan cututuka da ke da alaka da numfashi da ake kira The Lancet Respiratory Medicine ta fitar, ya ci gaba da cewa matukar aka sha daya daga cikin wadannan magunguna amma ba tare da ya kashe kwayoyin cutar ba a gaggauce, to akwai hatsarin cutar za ta rikide zuwa yanayin da sam ba ta jin magani.

A shekarar 2015 cutar tarin TB ta yi sanadiyyar mutuwar mutane milyan daya da dubu 800, mafi yawansu a kasashen India da Indonesia da China da Najeriya da Pakistan da kuma Sudan ta Kudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.