Isa ga babban shafi
EU

EU ta dauki tsauraran matakai kan dashen Nono

Majalisar Dokokin Tarayyar Turai ta dauki tsauraran matakan inganta harkar lafiya a dai dai lokacin da al’ummar duniya ke nuna farbaga kan matsalolin da ke tattare da dashen Nono.

Farbaga kan matsalolin da ke tattare da dashen nono
Farbaga kan matsalolin da ke tattare da dashen nono Reuters
Talla

Daukan matakan na zuwa ne bayan shafe kusan shekaru biyar ana tafka muhawara da zimmar tabbatar da ingancin na’urorin da ake amfani da su wajen dashen nono da kwankwaso.

Majalisar Dokokin wadda ta gudanar da zamanta a birnin Strasbourg na Faransa ta kuma amince da dokoki tsaurara kan na’urorin gwaje-gwaje cututtuka ko kuma rashin lafiya da suka hada da gwajin juna-biyu da gwajin gano kwayar halitta.

Daya daga cikin mambobin Majalisar Glenis Willmott ya ce, sun samar da matakai masu tsauri kan cibiyoyi da hukumomin da ke bada umarnin amfani da na’urorin kiwon lafiya.

Daga cikin matakan dai, za a bai wa marasa lafiya da likitocinsu damar bibiyar sinadaran da aka yi amfani da su wajen yi musu dashen.

Ana saran fara amfani da sabbin dokokin a tsakiyar shekarar 2020 mai zuwa.

A cikin watan Janairun da ya gabata ne wata Kotun birnin Toulouse da ke Fasransa ta bukaci cibiyar kula da ingancin kayayyaki a Jamus da ta biya diyyar Euro miliyan 60 ga mata dubu 20 da suka gamu da tangarda a dashen nonon da aka yi mu su, kuma cibiyar ce ta rattaba hannu don amincewa da ingancin na’urorin da aka yi mu su aiki da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.