rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

WHO Lafiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Yau ce ranar yaki da Zazzabin cizon Sauro

media
Cutar zazzabin Cizon Sauro na illa ga rayuwa musamman ta kananan yara. REUTERS/James Gathany

Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, Wato WHO, ta ce duk da nasaran da ake samu a yaki da Cutar Malaria, zazzabin na ci gaba da kasancewa babban barazana a duniya.


Ana dai gani akwai gazawar shugabanni wajen samun nasaran dakile cutar da ke lakume rayuka.

WHO ta ce daga shekarar 2001 zuwa yanzu, an samu nasarar hana kamuwa da cutar har sau miliyan 663 a yankin nahiyar Afirka kudu da hamadar Sahara, inda a nan ne ake samun kashi 90 cikin 100 na masu kamuwa da cutar.

Sai dai WHO ta ce zata sake gwada wani sabon maganin cutar malaria a kasashen Kenya da Ghana da Malawi wajen yiwa yara 360,000 rigakafi tsakanin shekarar 2018 zuwa 2020.

Kamfanin hada magungunan Birtaniya GlaxoSmithKline da kungiyar PATH suka samar da rigakafin.

Dakta Matshidiso Moeti, Daraktar shiya na hukumar ta bayyana cewar nasarar samun maganin riga kafin wani fata ne mai kyau a shirin da ake na dakile cutar da ke hallaka mutane da dama.

Jami’ar ta ce yana da muhimmanci ayi amfani da rigakafin tare da wasu dabarun hana kamuwa da cutar irin su maganin kashe .

Kasashen Afrika ne dai suka fi fama da cutar zazzabin cizon sauron, kuma yawancin wadanda ke mutuwa sakamakon kamuwa da ita yara ne.