rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Lafiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Masu kibar da ta wuce kima sun karu a duniya

media
Masu matsananciyar kiba sun karu a duniya REUTERS/Finbarr O'Reilly/Files

Wani sabon bincike da Mujallar Journal of Medicine ta wallafa na cewa kashi 1 cikin 10 na al’ummar duniya na fama da kibar da ta wuce kima, abin da ke haifar da cutuka da ke lakume rayukan miliyoyin jama'a.
 


Binciken da aka gudanar a kasashen duniya 195 a tsawon shekaru 35 ya bayyana cewa, alkalluman masu dauke da kiba sama da kima sun rubanya da kasashe 73 tun kaddamar da binciken a 1980.

A cewar Mujallar ta Jornal of Medicine, kibar da ta wuce kima na taka rawa wajen yaduwar cututtuka da ke zama barazana ga rayuwar al’umma.

A shekarar 2015, yara miliyan 107.7 aka bayyana cewa suna fama da irin wannan kibar, kana akwai manya miliyan 603.7 da kibarsu ta zarce kima a duniya.

Duk da cewa alkalluman kiba tsakanin yara bai zarce na manya ba, ana samun karuwa a tsawon shekaru 35 da aka dauka ana nazari a cewar rahoton.

An danganta mutuwar mutane sama da miliyan 4 a 2015  da kibar da ta wuce kima.

Cututtuka irin Ciwon siga da Kansa masu barazana ga rayuka, na saurin kisa ga masu kiba sama da kima a cewar dakta Christopher Murray, daya daga cikin jagororin binciken.