rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Lafiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Cututukan huhu sun hallaka mutane miliyan 3 da rabi

media
Kwaje-kwajen cututukan huhu a wani asibitin Faransa Getty Images/Owen Franken

Wani Binciken masana kiwon lafiya ya ce wasu kananan cututuka da ke kama huhu sun hallaka mutane sama da miliyan uku da rabi a shekarar 2015.


Rahotan binciken da aka wallafa a Mujallar kula da lafiya ta ce mutane kusan miliyan 3 da dubu dari 2 suka mutu sakamakon cutar da ke da nasaba da shan taba ko kuma gurbacewar muhalli, yayin da dubu dari 4 kuma suka mutu sakamakon cutar asthma.

Farfesa Theo Vos na Jami’ar Washington ya jagoranci wannan bincike wanda ya yi nazarin bayanan da aka tattara daga kasashe 188 na duniya wanda ya shafi wadanda suka kamu da cututukan da kuma wadanda suka mutu tsakanin shekarar 1990 zuwa shekarar 2015.

Kasashen da suka fi kamuwa da cutar da ke da nasaba da shan taba sun hada da Papua New Guinea da India da Lesotho da kuma Nepal, yayin da aka fi samun cutar asthma a Afghanistan da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Fiji da Kiribati da Lesotho da Papua New Guinea da kuma Swaziland.

Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce cutar da ke da nasaba da shan taba da kuma gurbacewar muhalli ita ce ta 4 wajen kisa a duniya a shekarar 2015, bayan cutar zuciya da ta kashe mutane miliyan 9 da shanyewar jiki da ta kashe mutane miliyan 6 sai kuma cutar da ke shafar numfashi da ta kashe miliyan 3 da dubu dari 2.