rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Lafiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shakar hayakin taba na sauya hanyoyin jinin huhu

media
Masu shan taba sun fi kamuwa da cutar kansar da wuri AFP PHOTO / GREG BAKER

Wani Binciken masana kiwon lafiya ya bayyana cewar shakar hayakin taba na sauya hanyoyin jinin huhu, abinda ke taimakawa wajen haifar da cutar sankara ko kansa.


Rahotan binciken da aka wallafa a Mujallar Cutar Kansa ta Amurka, ya biyo bayan binciken da aka gudanar kan masu shakar hayakin tabar na dogon lokaci ba tare da sun sha tabar ba.

Jagoran binciken Stephen Baylin, Darakta a Jami’ar Hopkins, ya ce masu shan taba sun fi kamuwa da cutar kansar da wuri, amma suma wadanda ke shakar hayakin ta ba tare da sun sha tabar ba, na iya kamuwa da cutar.

Baylin ya ce daina shan tabar na kuma rage saurin kamuwa da cutar baki daya.