rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Lafiya Ilimi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shan sigari na tattare da illa ga mai dauke da cutar HIV

media
Wasu mutane da ke busa sigari a birnin Mumbai na kasar India. REUTERS/Danish Siddiqui

Wani binciken masana kiwon lafiya yace mutanen dake dauke da sinadarin cutar kanjamau ko HIV dake shan taba na iya mutuwa sakamakon cutar sankarar huhu maimakon cutar ta kanjamau.


Binciken da aka wallafa a Mujallar kula da lafiya ‘JAMA’ ta Amurka, yayi gargadin cewa masu fama da cutar HIV dake zukar taba sigari na iya gaggauta samun sankarar huhu.

Rahotan yace zukar taba sigari na rage tsawon rayuwar mutanen dake fama da cutar HIV da kuma hana aikin maganin rage kaifin cutar.

Daya daga cikin wadanda suka rubta rahotan Krishna Reddy, likita a asibitin Massachussets dake Boston, yace akwai mummunar illa a tattare da hada cutar HIV da kuma zukar taba sigari.