rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Majalisar Dinkin Duniya Lafiya Mata

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Dabarun hana daukar ciki na karuwa a Karkara

media
Matan na rugumar tsarin kayyade Iyali a Karkara REUTERS/Afolabi Sotunde

Majalisar Dinkin Duniya ta ce amfani da hanyoyin hana daukar ciki na karuwa a Yankunan karkara wanda ke kare miliyoyin mata daga mutuwa wajen haihuwa kowacce shekara.


Bincike ya nuna cewar akalla mata da 'yan mata kusan miliyan 40 a fadin duniya ke amfani da hanyar zamani na hana daukar ciki sabanin yadda ake samu shekaru 5 da suka gabata musamman a kasashen Afirka da Asia da kuma kudancin Amurka.

Masana sun ce shirin kayyade iyali shine hanya mafi sauki wajen yaki da talauci tun da yana ragewa mata daukar nauyin iyalai masu yawa da kuma bai wa iyaye damar kula da yaran su sosai dangane da abinda ya shafi basu ilimi da kula da lafiyar su.

Rahotan Majalisar Dinkin Duniya ya ce amfani da kwaroron roba da kuma kwayoyin hana daukar ciki ya kare mata miliyan 84 wajen daukar cikin da basu shirya ba da kuma hana zubar da ciki miliyan 26 ta hanyoyi masu hadari, kana da kaucewa mutuwar mata 125,000 a shekarar da ta gabata.

Beth Schlachter, Babbar Daraktan Hukumar Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da rabin matan da ke amfani da irin wannan hanyar sun fito ne daga Asia, inda kashi 38 ke amfani da sabbin dabarun.

Rahotan ya ce a Afirka an samu karuwar matan da ke amfani da sabbin dabarun zamanin zuwa kashi sama da 23 daga kashi 19 da rabi da ake da shi tsakanin shekarar 2012 zuwa 2017.