rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kwallon Kafa Wasanni

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

FA na tuhumar Manchester City kan cinikin Jadon Sancho

media
Tsohon dan wasan Manchester City Jadon Sancho da ke taka leda a Borussia Dortmund NBC Sports/Getty Images

Hukumar kwallon kafar Ingila FA ta ce ta na bincike kan Haramtaccen biyan kudin da ake zargin ya faru tsakanin Manchester City da dillalin Jadon Sancho wato Emeka Obasi lokacin da ya kai mata dan wasan ya na da shekaru 14 da haihuwa.


Akwai dai bayanai da ke nuna cewa Man City ta biya Obasi yuro dubu dari biyu a shekarar 2015 wanda kuma ya sabawa dokokin hukumar FA kan cinikin kananun ‘yan wasan da basu kai shekaru 16 da haihuwa ba.

A ka’idar hukumar FA dai babu dillalin da ke da hurumin dillancin dan wasan da shekarunsa bas u kai 16 da haihuwa ba,

Jadon mai shekaru 18 yanzu a duniya, wanda ke taka leda da Borussia Dortmund ta Jamus, kafin yanzu Mancity ta saye shi ne daga Watford inda ta biya diyyar yuro dubu 66 ga Club din baya fa biyan Obasi yuro dubu dari 2 wanda ke matsayin dillalinsa.

Tuni dai Man City ta musanta zargin wanda ta ce wani yunkuri ne na bata sunan Club din.

Wata Mujallar wasanni a Ingila ta yi zargin cewa Emeka Obasi na matsayin dillalin da ke nemowa Man City kananun ‘yan wasa a nahiyar Turai da Latin Amurka ko da dai shima wannan zargi Club din ya musanta.