Isa ga babban shafi
Duniya

Yau ce ranar yaki da cutar Malaria a duniya

Yau ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin yaki da cutar zazzabin cizon sauro ko kuma Malaria, wanda ke haddasa asarar dubban rayuka a kowacce shekara.

Gidan Sauro na taka muhimmiyar rawa wajen yaki da cutar Malaria
Gidan Sauro na taka muhimmiyar rawa wajen yaki da cutar Malaria www.msf.org
Talla

Bikin na bana na zuwa ne a daidai lokacin da ake gwajin wani maganin riga-kafin kamuwa da cutar a Afirka.

Kasashen da ke yankin Kudu da Sahara sun fi fama da cutar Malaria wadda ta zama tamkar ruwan dare game duniya a yankin.

Kididdiga ta nuna cewa, mutane dubu 435 ne suka rasa rayukansu sakamakon cutar Malaria a shekarar 2017 a duniya, kuma kasashen da ke yankin Kudu da Sahara ne ke da kashi 93 cikin 100 na adadin wadanda suka mutun.

Najeriya ce kasar da ta fi yawan mutanen da cutar ta kashe , in da take da kashi 19 na wandanda suka mutu a duniya.

A yayin zanta wa da RFI Hausa a birnin Maiduguri, Dr. Mala Waziri, kwararren likita kuma shugaban yaki da Malaria a jihar ya ce, akwai bukatar jama’a su rika tsaftace muhallansu domin kare kansu daga cizon sauro.

Likitan ya ce, ruwan da ke zaune wuri guda na daya daga cikin abubuwan da ke haddasa yaduwar sauro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.