Isa ga babban shafi
WHO-Lafiya

Za a kammala kawar da Malaria daga duniya a shekarar 2050- WHO

Wata tawagar kwararru a fannin lafiya ta sha alwashin kawo karshen matsalar cutar Zazzabin Malaria da sauro ke haddasawa nan da shekarar 2050 mai zuwa ta hanyar hada hannu da hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya WHO.

Sauron da ke yada cutar Malaria mai kisa
Sauron da ke yada cutar Malaria mai kisa AFP/PHILIPPE HUGUEN
Talla

Bayan wani taron bita da tawagar kwararrun 41 tare da WHO suka gudanar sun bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta samu kwarin gwiwar iya magance cutar ta Malaria nan da shekarar 2050.

Cikin wani rahoto da WHO ta fitar ta nuna cewa cutar ta Malaria wadda ta addabi duniya tsawon lokaci ka iya bacewa a ban kasa ko da dai aikin kawar da ita na bukatar tarin kudi.

A cewar rahoton kafin yanzu yunkurin kawar da cutar Malaria na matsayin mafarki ga masana da kwararru a fannin kiwon lafiya, amma bayan binciken baya-bayan nan an samu kwarin gwiwar iya kawar da cutar dungurugum nan da shekarar 2050.

Sai dai a cewar Richard Feachem daraktan kungiyar Global Health a jami’ar California matukar ana bukatar nasara a bangaren dole ne sai an hada hannu da bangarori daban-daban fiye da duk wani nau’in hada hannu don kawar da wata cuta da aka taba yi a tarihi.

Rahoton WHO cikin makon nan ya bayyana cewa kawo yanzu babu adadin kudin da aikin zai lakume haka zalika ba a fayyace yawan hannun da ake bukata a aikin ba.

Akalla mutane miliyan 219 cutar Malaria ta kama cikin shekarar 2017 a duniya da adadi mai yawa a nahiyar Afrika inda kuma ta hallaka mutane dubu dari 4 da 35.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.