Isa ga babban shafi
WHO-Lafiya

WHO ta ayyana dokar ta baci kan cutar Coronavirus

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana dokar-ta-baci kan cutar Coronavirus wadda ke ci gaba da yaduwa a wasu kasashen duniya, yayin da kawo yanzu ta kashe mutane 213 a China.

Shugaban Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus
Shugaban Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus REUTERS/Denis Balibouse
Talla

Shugaban Hukumar Lafiyar ta WHO, Tedros Adhanom Ghebreysus ya ce, babban makasudin ayyana dokar ta bacin kan cutar Coronavirus a duniya, ba wai don abin da ke faruwa a China ba ne, illa don abin da ke fauwa a wasu kasashen duniya.

A na dari-darin cewa, wannan shu’ umar cuta ka iya bazuwa a kasashen da ke da raunin tsarin kiwon lafiya.

Tuni Amurka ta gargadi ‘yan kasarta kan balaguro zuwa China sakamakon cutar wadda ta aka tabbatar cewa ta lakume rayuka 213, yayin da ta harbi mutane kusan dubu 10.

Baya ga kasar China, Hukumar WHO ta ce, mutane 98 ne suka kamu da cutar a wasu kasashen duniya 18 amma kawo yanzu babu wanda aka tabbatar da mutuwarsa a kasashen.

Akasarin wadanda suka yi dakon cutar zuwa kasashensu, sun kwaso ta ne daga birnin Wuhan na China, wato mahaifar wannan cuta ta Coronavirus.

Kodayake rahotanni sun ce, an samu yaduwar cutar daga mutun zuwa wani mutun a kasashen Jamus da Japan da Vietnam da kuma Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.