Isa ga babban shafi
Lafiya

Za a yi wa yara miliyan 45 allurar Kyanda

Kungiyar bayar da riga-kafi ta Gavi ta sanar da shirin yi wa yara kanana miliyan 45 allurar riga-kafin kamuwa da cutar Kyanda a kasashen da ke yankunan Asiya da Afrika cikin watanni 6 masu zuwa.

Masu dauke da cutar Kyanda sun karu a duniya
Masu dauke da cutar Kyanda sun karu a duniya AFP PHOTO / GWENN DUBOURTHOUMIEU
Talla

Kungiyar ta ce, za ta yi aiki da gwamnatocin kasashen da abin ya shafa da  Hukumar Lafiya ta Duniya da Hukumar Kula da kuma Kananan Yara ta Duniya, UNICEF domin yi wa yaran 'yan kasa da shekaru 5 riga-kafin.

Seth Berkley Shugaban Kungiyar mai cibiya a birnin London ya ce, allurar ba ta da illa, kuma tana da inganci da kuma araha, yana mai cewa, babu dalilin da zai sa yara su rika mutuwa saboda cutar ta Kyanda.

Alkaluma sun nuna cewar, cutar Kyanda ta karu daga 360,000 da aka samu a shekarar 2018 zuwa 430,000 a shekarar 2019.

Kasashen da za su ci gajiyar riga-kafin sun hada da Bangladesh da Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya da Habasha da Kenya da Nepal da Somalia da kuma Sudan ta Kudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.