rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ministan sufurin Birtaniya ya yi murabus kan batun ficewar kasar daga EU

Ministan Sufurin Birtaniya Jo Johnson ya yi murabus daga mukaminsa tare da kalubalantar shirin ficewar kasar daga kungiyar tarayyar Turai.
Johnson wanda dan uwa ne ga Boris Johnson da ya yi Murabus daga mukamin sakataren harkokin wajen kasar cikin watan Yuli ya kuma bukaci sake gudanar da zaben raba gardamar ficewar kasar daga EU.