rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mutane 7 sun mutu a sabuwar zanga-zangar Iraqi

Akalla masu zanga-zanga 7 suka mutu yau asabar a Iraqi, yayinda jami’an tsaro suka tarwatsa filayen da dubban ‘yan kasar suka sake taruwa a biranen Bagadaza da Basra don ci gaba da zanga-zangar kin jinin gwamnati. Sabuwar arrangama tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zangar ta zo ne bayan da daukacin manyan jagororin siyasa da kusoshin gwamnati, suka cimma matsayar ci gaba da baiwa Fira Minista Adel Abdel Mahadi kariya daga masu boren dake neman tilasta masa yin murabus.