rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Georgia Afghanistan

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An kashe sojojin Georgia bakwai a Afghanistan

media
Wasu sojojin Afghanistan dake sintiri REUTERS/Omar Sobhani

Fadar Gwamnatin kasar Georgia, ta sanar da cewar an kashe sojojin kasar bakwai a harin kunar waken da aka kai musu a kasar Afghanistan.


Janar Irakli Dzneladze, hafsan hafsoshin sojin kasar, ya ce sojojin sun rasa rayukansu ne lokacin da wani Dan kunar bakin wake ya ta da bam a sansanin su.

Kungiyar Taliban wacce ke yaki da gwamnatin shugaba Hamid Karzai da dakarun NATO, ta dauki alhakin kai harin.