rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Kogi Abuja

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Dan sanda ya harbe direban Mota saboda na goro a Okene

media
Hanyar da ta hada kudanci da Arewacin Najeriya

Direbobin motocin dakon kaya dake zanga zanga a Najeriya sun datse wata babbar hanya da ta hada yankin kudanci da Arewacin kasar gab da kauyen Ozara a karamar hukumar Okene ta jahar Kogi arewa maso tsakkiyar tarrayar Najeriya.


Masu zanga-zangar dai sun bukaci a gurfanar da wasu yan sandan da suka kashe wani direban motar dakon kaya sakamakon kin basu cin hancin naira 100 da ya yi.

Idan dai ba’a manta ba al’amari makamancin hakan sun sha tayar da jijiyoyin wuya a tsakanin al’umma da jami’an yan sanda bisa karbar na goro, wannan na zuwa ne a yayin da sabuwar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ke kokarin kawar da matsalar cin hanci da rashawa da ya addabi  kasar.