Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ta tuhumi kamfanoni akan rashawa

Gwamnatin Najeriya ta tuhumi kamfanoni da wasu mutanen kasar fiye da 300 cikin su kuwa har da jami’an soji saboda ruf-da-ciki da kudaden da yawansu ya kai Naira biliyan 48 kamar yadda fadar shugaba Muhammadu Buhari ta sanar a ranar Alhamis. 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya lashi takobin yaki da cin hanci da rashawa a kasar.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya lashi takobin yaki da cin hanci da rashawa a kasar. statehouse
Talla

Shugaba Buhari da ya karbi ragamar kasar a bara, ya lashi takobin kawar da matsalar cin hanci da rashawa da ta jefa miliyoyin ‘yan Najeriya cikin talauci duk da arzikin man fetir da Allah ya hore wa kasar.

Buhari ya sallami tare da tuhumar wasu tsoffin jami’an gwamnatin Goodluck Jonathan da ta shude saboda cin hanci da rashawa, yayin da ya bayar da umarnin gudanar da bincike a manyan ma’aikatun kasar kamar kamfanin mai na NNPC.

Kwamitin bincike kan almundahanar da aka yi a ofishin tsohon mai bai wa shugaban kasar shawara kan harkokin tsaro ya ce, cikin wadanda aka tuhuma sun dawo da sama da Naira biliyan 7 ga gwamnatin tarayya, kuma ana sa ran na gaba, za su dawo da kudaden da yawansu ya kai Naira biliyan 41.

Kamfanonin da aka tuhuma dai sun karbi kwangila ne a ofishin Sambo Dasuki tsakanin shekara ta 2011 zuwa shekara ta 2014 yayin da wasun su suka ki yin aikin da yakamata su yi, sauran kuwa  ba su ma yi aiki ko guda ba duk da cewa sun karbi kudi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.