Isa ga babban shafi
Najeriya

Saraki ya sake shiga tsaka mai wuya

Wasu takardun sirri da ofishin alkalai ya fitar a kasar Panama sun nuna cewa iyalan gidan shugaban majalisar dattawan Najeriya Bukola Saraki sun boye akalla kadarori guda hudu a kasashen waje ba tare da sanin hukumomin Najeriya ba.

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Bukola Saraki.
Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Bukola Saraki. ynaija.com
Talla

Mr. Saraki bai bayyana wa kotun da ke kula da da’ar ma’aika ta Najeriya wadannan kadarorin ba duk da cewa dokar kasar ta bukaci ya yi haka.

Ana ganin wannan sabon tonon asirin da kungiyar ‘yan jaridu ta duniya ICIJ ta taimaka wajen watsawa zai kara jefa Mr. Saraki cikin tsaka mai wuya, lura da cewa yana kan kokarin wanke kansa daga zargin cin hanci da rashwa da ake yi ma sa.

Dokar kotun dai ta bukaci duk wani mai rike da mukamin siyasa da ya bayyana kadarorinsa da na matarsa da kuma kadarorin da aka mallaka da sunan ‘ya ‘yansa ‘yan kasa da shekaru 18. Amma Saraki bai sanar da wasu kadarorin ba kamar yadda sabon tonon asirin ya nuna.

Daga cikin kadarorin da iyalansa suka boye, sun hada da wata kadara da uwargidansa Toyin Saraki ta mallaka a birnin Landan wanda kuma shugaban majalisar dattawan bai sanar da kotun ba, abinda masharhanta ke kallo a matsayin karan tsaye ga doka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.