Isa ga babban shafi
Najeriya

An lalata bututun mai da muhimman kayayyaki sau 15,000

Babban Daraktan Kamfanin hakar man fetur na Najeriya NNPC, Dr Maikanti Kacalla Buru ya ce tsakanin shekarun 2010 zuwa 2015 tsagerun yankin Niger Delta sun lalata bututun mai da muhimman kayan hakar man sau 15,000. 

Gwamnatin Najeriya na kokarin kawo karshen fasa bututun mai
Gwamnatin Najeriya na kokarin kawo karshen fasa bututun mai
Talla

Baru ya bayyana wadannan alkalumma yayin da ya kai ziyara ofishin Kwamandan rundunar tsaro ta Civil Defence ta kasa Abdullahi Gana Muhammadu.

A cewar Babban daraktan na NNPC daga watan Janairu zuwa Mayu na 2016 tsagerun sun fasa bututun mai sau 1,447 lamarin da ya jawowa Najeriya hasarar litar albarkatun mai miliyan 109, da kuma hasarar gangar danyen man 560,000.

Baru ya kuma nuna damuwarsa bisa raguwar samar da iskar gas a tarayyar Najeriya da kashi 50%, saboda ta’addancin tsagerun Niger Delta, inda ya bukaci karin hadin gwiwar hukumar tsaron ta Civil Defence domin dakile wannan barna.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.