Isa ga babban shafi
Najeriya

An sake samun mai dauke da Polio a Najeriya

An sake samun yaro na Uku dauke da cutar Polio a Najeriya a wani al’amari da hukumar lafiya ta duniya, WHO, ke gargadi cewa akwai yiwuwar a samu wasu na gaba, wanda kuma ke sake kasance babban komawa baya a kokarin da ake na kawar da cutar baki daya a kasar.

Ana ci gaba da Rigakafin cutar Polio a Najeriya tun bayan sake bularta a arewacin kasar
Ana ci gaba da Rigakafin cutar Polio a Najeriya tun bayan sake bularta a arewacin kasar Getty Images/Ranplett
Talla

A wata sanarwa da Hukumar ta fitar, an samu yaron dake dauke da cutar ne a yankin Borno dake arewa maso gabashin Najeriya.

A watan Agusta aka samu yara biyu dake dauke da cutar shekarar daya bayan sanar da yin bankwana da Polio a kasar.

Najeriya dake kan hanyar tabbatar da cewa kafin shekarar mai zuwa babu Polio a kasarta, wananan a yanzu na sake tada hankali hukumomi a kokarin da ake na yaki da cutar dake shanye jinki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.