Isa ga babban shafi
Najeriya

An gargadi Najeriya kan shirin siyar da kadarorinta

Hadakar kungiyoyin kwadago a Najeriya ta bukaci gwamnatin kasar da ta yi watsi da shirinta na siyar da kadadorinta don kauce wa haddasa tashe-tashen hankula a kasar.

Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari REUTERS
Talla

Kungiyoyin da suka hada da NLC da TUC da NUPENG da PENGASSAN sun yi amfani da murya guda wajen gargadin gwamnatin kan shirin siyar da kadadorin.

Kawo yanzu dai, fadar shugaban kasar, Muhammadu Buhari ba ta ce komai ba game da wannan kiran, in da mai magana da yawun shugaban Femi Adesina ya ce, ba su da tacewa. 

Sai dai a ranar Asabar da ta gabata, ministan kasafi da tsare-tsare na kasar Udoma Udo Udoma ya fadi a cikin wata sanarwa cewa, gwamnatin ba za ta siyar da manyan kadarorinta ba, don farfado da asusunta na waje da kuma ceto tattalin arzikin kasar da ke cikin mawuyacin hali ba.

Dama tuni, NUPENG da PENGASSAN suka yi barazanar shiga yajin aikin game-gari don nuna adawa da shirin wanda suka ce, ba zai amfani talakawa ba illa wasu tsirarun mutane a Najeriyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.