Isa ga babban shafi
Najeriya

Rundunar Sojin Najeriya ta lalata haramtattun matatun mai 143

Rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar lalata matatun mai 143 da ake amfani da su wajen satar danyen mai a kuma fice da shi bayan tace shi a yankin Niger Delta.

Talla

Shugaban rundunar ta musamman da ke jagorantar yaki da masu lalata bututun mai da kuma sace shi Brigadier Janar Hassan Hamisu ne tabbatar da hakan.

Ya ce rundunar sojin ta samu wannan nasarar ce sakamakon kaddamar da wani sumame da tayi a yankin na Niger Delta inda bayan lalata haramtattun matatun man, suka samu nasarar tarwatsa sansanonin ‘yan ta’adda da dama da kawo yanzu basu bayyana yawansu ba.

Rundunar sojin Najeriya ta samu nasarori da dama kan ‘yan ta’adda a wasu jihohin kudu maso kudancin kasar tun bayan kaddamar da runduna ta musamman kan kawo karshen matsalar tsaro a yankin da a turance aka lakabawa “Operation Crocodile Smile”.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.