An saki yara 876 da ake tsare dasu a Najeriya
A Najeriya hukumar UNICEF ta tattauna da hukumomin tsaron kasar, hakan ya kai ga sakin yara 876, da aka jima ana tsare da su a wasu barikokin sojin kasar, bisa zarginsu da alaka da kungiyar Boko Haram.
Wallafawa ranar:
Darakatan hukumar ta UNICEF na yakunan yammaci da kuma tsakiyar Africa, Manuel Fontain, ya ce a baya Yaran su 876, suna zaune ne a yankunan da mayakan Boko Haram suka taba mamayewa.
A baya dai rundunar sojin Najeriya ta saki da yawa daga cikin yaran da take tsare da su bayan kammala bincike a kansu.
Amma a gefe guda hukumar ta UNICEF ta ce mai yiwuwa ne akwai wasu yaran da dama da ake tsare da su wasu barikokin sojin Najeriya da ke arewa maso gabashin kasar.
Har yanzu ba'a bayyana tsawon lokacin da yaran suka shafe a tsare ba, zalika ba'a bayyana ajin shekarunsu ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu