Isa ga babban shafi
Najeriya

Jam'iyyun adawa 16 sun bukaci dage zaben Gwamna a Jihar Ondo

Jam’iyyun Siyasa 16 a Najeriya, sun bukaci a dage zaben Gwamna a jihar Ondo da ke kudancin kasar, da za a yi a ranar 26 ga watan Nuwamba.

Alamun jam'iyyun siyasa da ke Najeriya
Alamun jam'iyyun siyasa da ke Najeriya
Talla

Kiran gamayyar jam’iyyun adawar na zuwa kwanaki kadan bayan da babbar jam’iyyar adawa a Najeriya PDP, ta bukaci da a dage zaben saboda dalilan tsaro.

Cikin wata takardar bayan taro da suka rattabawa hannu, Jam’iyyun adawar sun ce kiran ya zama tilas, saboda kaucewa aukuwar kazamin rikicin siyasa a jihar ta Ondo, idan har aka gudanar da zaben na Gwamna kamar yadda aka tsara.

Jam’iyyu 16 sun kunshi, ADC, PPA ACPN, BNPP, DPC, da kuma DPP.

Sauran Jam’iyyun sun kunshi, NCP, PDC, LP, PPN, UDP, ACD, PPP, PRP, UPP da kuma ID.

Yanzu haka Najeriya na da Jam’yyun siyasa 29 da aka yiwa rijista, kuma 28 ne zasu fafata a zaben.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.