Isa ga babban shafi
Najeriya

Za'a tura dubban jami'an 'yan sanda zuwa Ondo

Rundunar ‘yan sandan Najeriya, ta ce zata tura jami’anta 26,000, jirage masu saukar Ungulu 3, motocin Sulke 12, da kuma kananan jiragen ruwa na tsaro, zuwa jihar Ondo, domin tabbatar da kwanciyar hankali, yayin gudanar da zaben Gwamna.

Jami'an rundunar 'yan sanda ta Najeriya
Jami'an rundunar 'yan sanda ta Najeriya
Talla

Sifeto Janar na ‘yan sandan Najeriya Ibrahim Idris ya sanar da haka yayin wani taro tsakaninsa da Jami’an hukumar shirya zaben kasar INEC, da kuma Jam’iyyun Siyasa.

Sifeto Janar Idris, ya ce za’a tura jami’an ‘yan sanda 5 zuwa kowane akwatin zabe da ke jihar, yayin gudanar da zabe. Sifeto Janar din ya kuma kara da cewa kananan jiragen tsaro 20 za’a tura zuwa yankunan da suka yi iyaka da ruwa, domin dakile yunkurin ‘yan ta’addan yankin Niger Delta na tada zaune tsaye.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.