Isa ga babban shafi
Najeriya

‘Yan sanda sun cafke barayin mutane a Najeriya

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta sanar da kama wasu mutane uku da ake tuhuma da garkuwa da wasu ma’aikatan kamfanin Dangote ‘yan kasashen waje guda biyar, da kuma kashe wani manajan kamfanin da ya kai musu kudin diyya sama da naira miliyan 5 da rabi.

‘Yan sanda Najeriya sun cafke wasu barayin mutane uku.
‘Yan sanda Najeriya sun cafke wasu barayin mutane uku. AFP PHOTO / Quentin Leboucher
Talla

'Yan fashin sun hada da Abubakar Gide mai shekaru 24 da Abdullahi Salihu mai shekaru 22 da kuma babuga Adamu mai shekaru 25.

Kakakin ‘Yan Sandan Don Awunah ya ce an kama Gide ne a Ijebu Igbo dake Jihar Ogun, yayin da aka kama Salihu a wani dajin Epe dake Lagos sai kuma Adamu a Jihar Kwara.

Matsalar satar mutane da kuma neman kudin fansa ya zama ruwan dare a Najeriya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.