Isa ga babban shafi
Najeriya

Yunwa ta hallaka mutane 2,000 a arewa maso gabashin Najeriya

Wata cibiyar bincike da ke Amurka ta ce yawan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon yunwa a yankin arewa maso gabashin Najeriya mai fama da ayyukan Boko Haram ya haura mutane dubu biyu a bana kawai.

Mutane sama da miliyan biyu rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu a arewa maso gabashin Najeriya.
Mutane sama da miliyan biyu rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu a arewa maso gabashin Najeriya. AFP PHOTO/STRINGER
Talla

Cibiyar mai suna Early Warning Systems Network, ta ce yanzu haka akwai dubban mutane da ke fama da yunwa sannan kuma suke bukatar taimakon gaggawa a yankin da ya sha fama da rikicin Boko Haram.

An tafka asarar rayuka a garin Bama fiye da sauran garuruwan da kungiyar Boko Haram ta karbe iko a jahar Borno.

Binciken ya kuma ce akwai yiyuwar wasu yankunan jahar za su fuskanci matsanancin yunwa ganin matsalar da ake fuskanta wajen isar da kayyakin agaji.

Mutane fiye da miliyan hudu na da bukatar agajin gaggawa a jihohin Borno da Adamawa da Yobe sai dai mafi yawansu na tsugune ne a jahar Borno acewar binciken.

A wannan shekarar bayan inganta tsaro a wadanan yankunan an sami shiga da kayyakin agaji sai dai akwai yankunan da aka gagara shiga sanadiyar rikicin Boko Haram .

Mutane dubu goma sha biyar ne suka mutu yayin da wasu fiye da miliyan biyu suka rasa matsuguni a shekaru bakwai da aka kwashe ana fama da rikicin Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.