Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya na neman jami'an Kwastam ruwa a jallo

Hukumar hana fasa kauri ta Najeriya wato Kwastam na neman biyu daga cikin manyan jami’anta da ke da hannu wajen safarar manyan bindigogi 661 cikin kasar.

Manyan jami'an Kwatam da ake nema ruwa a jallo a Najeriya
Manyan jami'an Kwatam da ake nema ruwa a jallo a Najeriya http://politicsngr.com
Talla

Sanarwar da hukumar ta bayar ta bayyana Abdullahi I. mai lambar aiki 44483 ASC da kuma Odiba Haruna Inah mai lambar aiki 133386 ACIC a matsayin jami’an da ake nema ruwa a jallo.

Mataimakin Kwantirola Janar, Dan Ugo ya bada umurnin kama mutanen biyu a duk in da aka gan su, yayin da tuni aka cafke mutane uku da ake zargi da hannu wajen shigo da makaman.

An dai kama makaman ne a birnin Legas, in da aka boye su a tsakan-kanin kofofi na karfe don shiga da su cikin sauki.

Shugaban hukumar kwastam ta kasar Kanar Hamid Ali ya ce, an haramta shigo da irin wadannan makaman, sannan kuma an shigo da su ba bisa ka'ida ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.