Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya za ta biya bashi ga mayakan Niger Delta

Gwamnatin Najeriya ta ce, nan gaba kadan za ta biya basukan da tsoffin 'yan tawayen Niger Delta ke bin ta daga cikin kudaden da ake biyan su, a karkashin yarjejeniyar ahuwar da suka kulla da gwamnati a shekarar 2009. 

Gwamnatin Najeriya za ta biya basukan da tsoffin mayakan Niger Delta ke bin ta
Gwamnatin Najeriya za ta biya basukan da tsoffin mayakan Niger Delta ke bin ta (Photo : Pius Utomi Ekpei/AFP)
Talla

Ofishin kula da biyan tsoffin 'yan tawayen ya bukace su da su kara hakuri kadan domin gwamnati na shirin biyan su kudaden watannin baya da suka wuce.

Akalla kowanne mutum guda na karbar Naira dubu 65 a kowanne wata.

Dakatar da shirin a baya ya sanya matasan kaddamar da hare-hare kan bututun mai, abin da ya sa man da Najeriya ke fitarwa ya ragu daga ganguna kusan miliyan 2 zuwa ganguna dubu 700 a kowacce rana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.