Isa ga babban shafi
Najeriya

An yi bikin sasanta makiyaya da manoma a Zamfara

An gudanar da wani bikin sasanta makiya da manoma da kuma masu kwashe shanun jama’a a jihar Zamfara da ke arawacin Najeriya, bikin da ya samu halartar shuagbanin siyasa da na tsaro da kuma sarakunan gargajiya.

An yi sulhu tsakanin Fulani makiyaya da manoma a jihar Zamfara
An yi sulhu tsakanin Fulani makiyaya da manoma a jihar Zamfara Veronique DURRUTY/Gamma-Rapho via Getty Images
Talla

Wannan ya biyo bayan aikin da kwamitin zaman lafiya a karkashin mataimakin gwamnan jihar Ibrahim Wakalla ya yi don sasanta bangarorin da ke rikicin da ya lakume daruruwan rayukan jama’a.

A hirarsa da RFI hausa, Alh Sani Gwamna, daya daga cikin mambobin kwamitin, ya ce, masu rikicin sun yafe wa juna, sanna kuma sun yi alkawarin ajiye makamai.

Gwamna ya ce, yanzu haka Fulani ba sa fargabar zuwa kasuwanni ko kuma masallacin jumma’a saboda sulhun da aka yi musu tsakaninsu da ‘yan sa-kai da ke kai musu farmaki a duk in da suka gan su.

A can baya dai, Fulanin na dari-darin zuwa kasuwanni ko kuma masallacin jumma’a saboda rashin zaman lafiya tsakaninsu da ‘yan sa-kai, amma yanzu an shawo kan matsalar, kamar yadda Sani Gwamna ya tabbatar mana.

Gwamna ya kara da cewa, jama’a da dama na iya zuwa daji don yin itace ko kuma kiwo ba tare da fuskantar wata barazana saboda zaman lafiyar da aka samu a yanzu a jihar ta Zamfara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.