Isa ga babban shafi
Najeriya

Rundunar sojin Najeriya ta musanta kisan 'yan kungiyar IPOB

Rundunar sojin Najeriya ta ce ba zata cigaba da lamuntar yi mata kazafin cewa tana cin zarafin dan adam ba, daga kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra wadda aka fi sani da IPOB.

Wasu 'yan kungiyar IPOB masu ra'ayin kafa kasar Biafra
Wasu 'yan kungiyar IPOB masu ra'ayin kafa kasar Biafra naijagists.com
Talla

Rundunar sojin ta maida martani ne kan sanarwar da wani kakakin kungiyar ta IPOB Emma Powerful ya fitar, cewa jami’an sojin Najeriya sun harbe wasu ‘yan kungiyar ta IPOB 11 a ranar 20 ga watan janairun da ya gabata, yayinda suke gudanar da zanga zangar nuna goyon bayansu ga nasarar da Donald Trump ya samu na zama shugaban Amurka.

Kakakin rundunar sojin Najeriya ta 6 da ke birnin Fatakwal, Kanal Aminu Iliyasu ya ce baki dayan sojojin da aka girke a titunan birnin na Fatakwal, basu harba ko da harsashi guda ba a lokacin zanga zangar, duk da tsokanar fada da suka rika yi, dan haka zargin na kungiyar IPOB masu ra’ayin Biafra bashi da tushe.

Kanal Aminu ya ce a ranar ta 20 ga watan Janairu, ‘ya’yan kungiyar ta IPOB sun yo fitar dango daga jihohin Abia, Anambra, Enugu, Imo da kuma Cross River don zanga zangar da nufin cin zarafin mutanen gari da babu ruwansu, hadi da matafiyan da ke ratsa birnin na Fatakwal, abinda ya jefa rayukan jama’a cikin hadari.

Kakakin ya kara da cewa bayanda masu zanga zangar suka fara jifan jami’an tsaro da duwatsu ne, ‘yan sanda suka yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.