Najeriya: Yawan wadanda suka rasu sakamakon cutar Sankarau ya karu
Mai’aikatar lafiya ta Najeriya, ta ce yawan wadanda suka rasa rayukansu a dalilin barkewar cutar sankarau a sassan kasar ya karu 328, daga cikin mutane 2,524 da suka kamu da cutar.
Wallafawa ranar:
Daraktan yada labaran ma’aikatar lafiyar, Boade Akinola ya ce alkalummansu na nuni da cewa kananan hukumomi 90 annobar ta shafa a johohi 16 da ke Najeriya, Jihohin sun hada da Kano, Katsina, Zamfara, Kebbi, Niger, Abuja, Osun, Cross Rivers, da kuma Legas.
Sauran jihohin da cutar a bulla sun hada da Nasarawa, Taraba, Jigawa, Filato, Yobe, Sakwato da kuma Niger.
Zalika ma’aikatar lafiyar ta ce, annobar ba ta tsaya kawai a Najeriya ba, cutar ta sankarau ta bulla a kasashen Niger, Chadi, Kamaru, Togo da kuma Burkina Faso.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu