Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotu ta ba da belin Sule Lamido

Kotun da ke sauraron karar da aka shigar gabanta kan tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ta bayar da Belinsa a yau Alhamis bayan shafe kwananki 4 ana tsare da shi.

Tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido bayan bayar da belinsa
Tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido bayan bayar da belinsa RFIHAUSA\DANDAGO
Talla

Alkalin Kotun da ke zamanta a Dutse, Usman Muhammad Lamin ya bayar da Belin Lamido ne a bisa aminta da kimarsa ta shugaban al’umma da kuma rashin gamsasun hujojjin ci gaba da tsare shi.

Rundunar 'Yan Sandan Najeriya, Shiya ta daya da ke Jihar Kano ce ta gurfanar da tsohon gwamnan kan laifuka hudu, da suka hadar da ingiza Jama'a, da bata sunan gwamna Mai ci, sai kuma barazana ga zaman lafiya.

Zarge-zargen da tsohon gwamnan ya musanta. Jam'iyyar PDP a Jihar Jigawa na zargin cewar ana yiwa Sule bita da kullin siyasa ne.

Wakilinmu Abubakar Issa Dandago ya rawaito cewa alkalin ya tsayar da ranar 5 ga watan 7 domin ci gaba da shara’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.