rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Hakkin Dan Adam

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

‘Yan Najeriya 300 ke jiran aiwatar musu da hunkuncin kisa a ketare

media
‘Yan Najeriya 300 ke jiran aiwatar musu da hunkuncin kisa a kasashen Asia ALABAMA

Gwamnatin Najeriya ta ce abu ne mai wuya kasashen da suka yankewa 'yan Kasar hukuncin kisa saboda safarar miyagun kwayoyi su amince da shirin musayar firsinoni da ita.


Ministan harkokin waje Geoffrey Onyeama ya bayyana haka, yayin ganawa da wata kungiyar kare Hakkin Bil Adama da ke neman ganin an ceto ‘Yan Najeriya sama da 300 da yanzu haka ke jiran aiwatar musu da hunkuncin.

Kungiyar ta bayyana cewar, Yanzu akwai ‘yan kasar 120 a China da ke jiran aiwatar da hukuncin, bayan wasu 170 da ke kasashen Indonesia da Malaysia da Vietnam da Qatar da Daular larabawa da kuma Saudi Arabia.

Kungiyar ta kuma ce ‘Yan Najeriya 16,500 ke tsare a gidajen yarin duniya.