Isa ga babban shafi
Najeriya

Dalilan da suka yi tasiri kan sakin karin 'yan Chibok

Wata majiya da ke kusa da mayakan Boko Haram ta bayyana cewa, gwamnatin Najeriya ta yi musayar ‘yan matan Chibok 82 da wasu kwamandojin kungiyar guda uku.

Hoton bidiyo marar motsi da ke nuna 'yan matan Chibok da aka sako a baya-bayannan, suna zaune ne a wani dakin taro a babban birnin Najeriya Abuja.
Hoton bidiyo marar motsi da ke nuna 'yan matan Chibok da aka sako a baya-bayannan, suna zaune ne a wani dakin taro a babban birnin Najeriya Abuja. REUTERS
Talla

Wannan na zuwa ne bayan ma su shiga tsakani, sun shafe akalla makwanni shida suna jagorantar yarjejeniyar musayar tsakanin bangarorin biyu kamar yadda Kamfanin Dillacin Labaran Faransa AFP ya rawaito,

Rahotanni sun ce, murkushe Boko Haram da kuma tsagewar kungiyar gida biyu gami da rashin lafiyar shugaban Najeriya Muhd Buhari sun taimaka wajen sakin ‘yan matan na Chibok 82 da suka shafe fiye da shakaru uku a hannun mayakan Boko Haram.
Majiyoyin tsaro sun ce, an mika ‘yan matan ne ga wasu jami’an kungiyar bada aaaji ta Red Cross a wani daji da ke kusa da garin Banki, a kan iyakar Najeriya da Kamaru.

Majiyoyin sun kara da cewa, an yi ta samun kwan –gaba kwan-baya tsakanin gwamnatin Najeriya da Boko Haram kafin cimma yarjejeniyar musayar.

Kamfanin Dillancin labaran Faransa na AFP ya rawaito majiyoyin na cewa, Abubakar Shekau ya rasa kwamandojinsa da dama a wani farmaki da aka kai wa gangaminsu a ranar 28 ga watan Afrilu a kauyen Balla, abin da ya sa ya bukaci maye gurabensu da wasu mayakan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.