rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Ilimi Hakkin Dan Adam

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Watanni 9 ba a biyan malaman makaranta a Bayelsa

media
Gwamnan Jihar Bayelsa Seriake Dickson Wordpress.com

Malaman Makarantu a Jihar Bayelsa da ke Najeriya sun kaddamar da wani yajin aikin gama gari, saboda abinda suka kira kin biyan su albashi na watanni tara da rabi.


Malaman sun ki amincewa da tayin da Gwamnatin Jihar ta yi musu na karbar albashin wata guda dan kaucewa yajin aikin.

Shugaban kungiyar malaman, Kalama Toinpre ya ce zasu ci gaba da kauracewa azuzuwa sai Gwamnatin Jihar ta biya su akalla albashin watanni uku.

Toinpre ya kuma bukaci malaman da su gudanar da azumi da addu’oi na kwanaki 7 dan samun taimakon Ubangiji.