rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Lafiya Ebola

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Najeriya: Ana daukar matakan kariya bayan sake bullar cutar Ebola

media
Ebola ta sake bulla a jamhuriyyar Dimokaradiyyar Congo. congovoice.org

Ministan lafiyar Najeriya, Isaac Adewole, ya umarci kafatanin ma’aikatan lafiya da al’ummar kasar su kasance cikin taka tsantsan da lura da duk wanda ya kamu da alamun zazzabi mai zafi a tsakaninsu, don shaidawa ma'aikatan lafiya mafi kusa.


Ministan ya bada umarnin ne, bayanda hukumar kula da lafiya ta duniya WHO, ta tabbatar da sake bullar cutar Ebola a Jamhuriyyar Dimokaradiyyar Congo.

Daga cikin alamun kamuwa da cutar dai akwai, zazzabi mai zafin gaske, jiri, da rashin karfin jiki, idan kuwa cutar ta girmama tana haifar da fitar jini ta baki, kunne da kuma kafofin fata.

Tuni dai cibiyar dakile yaduwar cututtukan Najeriya, ta bayyana cewa tana zaune cikin shirin ko ta kwana, domin tarar duk wata barazanar sake bullar cutar ta Ebola a kasar.