Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta yi wa ‘yan gudun hijira ‘yankar Rago

An Gudanar da jana’izar wasu ‘yan gudun hijira 4 da mayakan Boko Haram suka yiwa yankar rago a Dalori da ke Jihar Barnon Najeriya.

Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau
Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau AFP Photo/Boko Haram
Talla

Rahotanni sun ce ‘yan gudun hijirar 4 da aka yanka suna zama a sansanin Dalori ne, kuma sun ci karo da mayakan ne lokacin da suke farauta a daji.

Mayakan Boko Haram na ci gaba da kai hare hare a wasu sassan Jihar Borno duk da nasarar da sojojin Najeriya suka samu na tarwatsa su.

Ko a makonnin ba ya sai da suka yiwa wasu manoma yankar rago a dai-dai lokacin da suke gudanar da ayyukan gonanakin su a kauyen Maiduguri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.